Wallahi da in auri Talaka gara in mutu ban yi aure ba—Fateema Sheka

Gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umaru Radda ya kaddamar da motocin yaki na sulke da motoci 64 kirar Hilux da babura 700 da jami’an tsaron sakai 1,466 da ya dauka don kawo karshen matsalolin tsaron da ya addabi jihar Katsina.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da sabbin jami’an tsaro 1,466 da aka dauka aiki a Katsina Community Watch Corps. Rundunar za ta hada kai da jami’an tsaro da ake da su domin karfafa kokarin yaki da miyagun yan ta’adda da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Gwamnan, a yayin bikin, ya mikawa rundunar da jami’an tsaro da ke aiki a jihar motoci kirar Toyota Hilux guda 64, babura guda 700, makaman yaki da na’urorin sadarwa.

Babu shakka, wannan cika alkawari ya nuna jajircewar gwamnatin jihar Katsina wajen magance matsalar rashin tsaro ta hanyar sabbin hanyoyin warware matsalolin da suka shafi al’umma.

Muhimman mutanen da suka halarci taron mai dimbin tarihi sun hada da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, gwamnonin jihohin Kano, Kebbi, Zamfara, Sokoto da Yobe, sarakunan Katsina da Daura, darakta janar na hukumar leken asiri ta kasa NIA, Ahmad Rufa’i., Ministan gidaje da raya birane, Arch. Ahmad Musa Dangiwa, da sauransu.

Isah Miqdad AD Saude
SSA Digital Media to the Executive Governor of Katsina State.

Views: 12

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *