Rahotanni daga jihar Imon Najeriya na cewa ƴan sanda sun kama wasu ƴan mata waɗanda basu wuce shekaru 17 ba da laifin yin cikin shege.
A wani labarin kuma.
Daga shafin Datti
‘YAN HAUSA FILM SUNA NEMAN WUCE IYAKA

Wannan sakon ya shafi bangaren su jarumin Hausa film Adam A. Zango da bangaren su S. Bono
An ja hankalina bisa wasu munanan wakoki na fitsara da rashin albarka da suka fitar tare da wasu ‘yan mata sanye da wanduna damammu babu dan kwali a kansu, sun sanya gashin doki sai kace ba ‘ya’yan Musulmai ba
S. Bono kace kai Malami ne ko Dalibin Ilimi, ka taba koyarwa a Islamiyya, amma saboda neman duniya ta hanyar da bata dace ba ke jefar da Maluntar naka, ka nemo ‘yar mutane ka sata rawa da waka babu dan kwali a kanta kuma tana sanye da wando
Zan bada Misali da fim din Izzar So, tauraruwar film din mai sun Nana tana burge mutanen kirki, saboda kullun tana cikin hijabi tana jan ayoyin Qur’ani da Hadisai, kun sa ta tana koyar da dabi’u na kwarai a film din
Amma gashi nan daga karshe kun rusa mata martaba da kamala, kun sakata cikin waka na iskanci babu dan kwali a kanta tana sanye da wando damamme
Abinda ku keyi wuce makadi da rawa ne, fitsara ne zalla da rashin kunya, na tabbata ba zaku iya aikata haka da ‘ya’yan cikin ku ba, yanzu kai tsaye kun koma kwaikwayon abinda turawa da yahudaa sukeyi, kuma kunce kuna koya mana tarbiyya ne
Muna kira ga hukumomi masu sanya ido akan ‘yan film da mawaka, ya kamata a takawa abinda su Adam A. Zango, S. Bono Hamisu Breaker sukeyi a cikin wakokin fitsara
Muna fatan Allah Ya shiryar da su
Views: 16
