Yadda zaka gane cewa matarka na sonka da gaske ba da wasa ba

Yadda zaka gane cewa matarka na sonka da gaske ba da wasa ba

Ba za ka san matarka na sonka ba sai ka gaya mata za ka yo mata kishiya ko da kuwa da gangan ne.

In ta shanye ta mazaye toh barkanka ka rik’eta da kyau hannu bibiyu. In kuwa son da take nuna ma na boge ne to gaskiya za ta bayyana.

Akwai sahihan mata ba wai babu ba wAllaahi amma mafi akasarinsu ba sa iya ‘boye hali ko irin zaman da su ke yi da kai a zance k’ara aure.

Kuma ba ga wacca ba ta yi karatu ba ba ga malama ba. Kar kuma ka ce y’ar boko ta waye da ilimi don haka ba za ta damu ba samsam ba haka ba ne. Mace mace ce illa kawai k’alilan.

Ni babban abin da ke bani mamaki shi ne yadda mace za zauna da mijinta tana sane d’an yankan kai ne, d’an fashi da makami ne, d’an kidimashin ne, d’an 419 ne, d’an luwadi ne, mai neman matan banza ne da dai sauransu amma ba za ka ji ta ce bihim ba.

Sai dai da zarar ya ce zai auri wata don buk’atar hakan ta taso sai ta ce allanfur munafiki ne shi maci amana!

Jama’a don Allaah ko da wanda ko wacca za ta iya ganar da ni wannan lamari. wAllaahi ba zolaya nake ba da gaske nake neman wannan fahimta.

Views: 112

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *