
Rahotanni daga sashin Hausa na BBC na cewa yan sanda sun kama Abduljabbar kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya gaya BBC cewa sun gurfanar da Sheik Abduljabbar a gaban kotun Kofar Kudu da ke kwaryar Birnin Kano a ranar Juma’a, bisa zargin ɓatamci ga addini da kuma tunzura jama’a.
A cewarsa tuni alƙali ya aike da shi gidan yari.
Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya fitar ta ce an gurfanar da Malamin ne, “wanda ya yi ƙaurin suna wajen ɓatanci ga manzon Allah da kuma Sahabbansa”, bayan da aka samu rahoton farko daga wurin ‘yan sanda da kuma ofishin kwamishinan shari’a wadanda suka shirya tuhume-tuhumen da ake yi wa Malamin.
©BBC Hausa
Views: 29
