
Gwamnatin jihar Katsina a kar kashin jagorancin mai girma gwamna Aminu Bello Masari, ta sanar da cewa za ta mayar da gidajen kallo makarantun islamiyya a fadin jihar.
Wani dan majalissar dokokin jihar ta Katsina ne dai ya gabatar da wannan kuduri a zauren majalissar dokokin jihar, bayan majalissar ta duba sannan ta tabbatar da zar tas da kudurin kafin daga bisani gwamnan jihar ya sa hannu a kan kudurin.
Hukuncin dai zai shafi gidajen kallon da gwamnatin jihar ta gina domin haska wasanni, daga yanzu za’a rufe su a daina kallo kwata kwata, inda a mai makon haka za’a rika koyar da yara karatun islamiyya.
Views: 26
