Inna lillahi wa inna lillahin raji’un, Allah ya zare ransa lokacin da yake wa addini hidima

INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJI’UUN!

Shehin malami ya rasu yana yi wa addinin musulunci hidima

Shugaban Jama’atul Nasrul Islam na jihar Sokoto Mallam Abubakar (Ubandoman Gudu) ya rasu

Cikin jimami da kaduwa nake sanarda ku rasuwar babban Malamin addinin musulunci kuma daya daga cikin iyayena Mallam Abubakar Sulaiman(Ubandoman-Gudu).

Malam Abubakar Sulaiman shine shugaban Jama’atul Nasrul Islam, wanda kusan ya gama rasuwar ne ta hanyar yi wa addinin musulunci hidima.

Ubandoma mutun ne mai hakuri da juriya. Mutun ne wanda baka taba ji ko ganin abokin fadar sa ba. Shi a kulum babu abin da ya sanya a gaba illa ganin ya taimaki addanin musulunci ya ci gaba.

Na rantse da Allah ban san adadin ya’yan musulmi daya tarbiyyantar tare da basu ilimin addinin musulunci ba. Dudda yawan shekarun sa idan akace hidimar addinin musulunci ta taso sai ka ganshi a sahun gaba.

Hakika mun tafka babban rashi, kuma muna rokon Allah ya biya shi da gidan aljanna madaukakiya.

Daga: S-bin Abdallah Sokoto

LABARAI MASU ALAKA:

Views: 19

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *