Wani faI Fan bidiyon da bai wuce dakika 30 ba ya nuna yadda jami’in tsaron Najeriya suka kama yan bindigar da suka addabi jihohin Katsina Kaduna da Zamfara ku kalli bidiyon.
A wani labarin
Matakan da mu ka dauka sun tursasama “yan bindiga mika wuya ~ Matawalle
A cewarsa, mutanen da aka sace kuma su ka shafe makonni ko ma watanni a hannun masu garkuwar yanzu sun fara dawowa gidajensu su kuma ’yan bindigar na guduwa su na barin baburansu bayan man cikinsu ya kare.
Gwamna Matawalle ya ce “Babban Hafsan Sojin kasa ya ziyarci Jiharmu don duba lamarin.
Sojoji da kuma ’yan sa-kai na yankunan na can su na iyakar kokarinsu a dazuka domin zakulo ’yan bindigar.
“Kazalika, sojoji na ci gaba da kai munanan hare-hare yanzu haka Kuma nan ba da jimawa ba za mu tarwatsa dukkansu.
Gwamnnan ya kara da cewar Babu inda zan je zan zauna a jihar tsawon wannan lokacin da za a dauka ana aikin.
Dole nima na ji abin da kowa ke ji musamman na katse hanyoyin sadarwa.
A cewarsa mun kafa shingayen bincike a duk tsawon kilomita biyar a fadin jihar ta yadda babu wani 6ata-gari da zai kai labari.
Views: 49
