
Duk da irin tsamin rashin tsaron da ake fama da shi a ƙasar nan da koma bayan tattalin arziki hakan bai hana wasu daga cikin magoya bayan shugaba Buhari nuna soyayyarsu gare shi ba.
Shahahararren mawaƙin siyasar nan Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya bayyana cewar har yanzu bai ga mutumin da ya kai Buhari, gaskiya ba a kaf faɗin tarayyar Nijeriya.
Inda har ya ce idan don ta shi ne bai ƙi a ƙarawa shugaban wa’adin shekaru biyar nan gaba ba domin ya samu damar ƙarasa ayyukan alherin da ya soma.
Views: 9
