
Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta sake yin fatali da buƙatar bayar da belin dakataccen mataimakin kwamishinan ƴan sanda, Abba Kyari.
Kyari na neman kotun ta soke hukuncin farko da wata babbar kotu a Abuja ta yi wadda ta ƙi ta amsa buƙatarsa ta neman beli.
Alƙali Stephen Adah, wanda ya karanta hukuncin tawagar alƙalan uku, ya yanke cewa la’akari da irin tuhume-tuhumen da ake yi wa Abba Kyari a gaban kotu, dole a yi taka tsan-tsan da buƙatar ba shi beli.
Ya ce alƙali Emeka Nwite na babbar kotun Abuja, wanda tun farko ya yi watsi da bukatar belin ta Kyari, ya yi amfani da damarsa ta ƙin bayar da belin.
Hukumar NDLEA da ke yaki da sha da safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya ce take tuhumar Kyari wanda shi ne tsohon jagoran tawagar kai ɗauki ta musamman ta ‘yan sanda kan bayanai na sirri, Police Intelligence Response Team (IRT).
An tuhumi Kyari da wasu mambobin IRT – ACP Sunday J. Ubua da ASP Bawa James da Sufeto Simon Agirgba da Sufeto John Nuhu da haɗa baki kan ta’ammali da hodar iblis.
source: bbchausa
Views: 12
