An kama mutumin daya zagi Matar MANZON ALLAH SAW a brnin Makka

Masarautar Zazzau zata gina masallacin juma’a mafi kyau a faɗin Arewacin Najeriya

Masarautar Zazzau ƙarƙashin maimartaba Mal. Amb. Dr. Ahmad Nuhu Bamalli (CFR) ta ƙaddamar da sabon taswiran gina sabon babban masallacin juma’ar na birnin zariya na malam Abdulkarim wanda za a fara aiwatar da aikin nasa nan kurkusa.”

Bugu da ƙari sake gina babban masallacin juma’a ɗin yana da nasabar rushewar wani ɓangare na masallacin wanda har ya jawo asarar rayuka na mutum 8 tare da jikkata wasu ba’adi mahalarta sallar la’asar a ranar juma’ar da ta gabata.”

Manya-manyan baƙi ne daga sassa daban-daban a Nijeriya zasu halarci wannan babban taron da zai gudana a yau Asabar insha Allahu.”

Za’a gudanar da babban taron ƙaddamar da taswiran gina sabon masallacin ne a yau asabar 14/October/2023 da mislalin 11:00am a babban ɗakin taro na shehu musa ‘yaradua dake babban birnin tarayya Abuja.”

Views: 9

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *