Inna Lillahi Wa’inna Ilaihin Raji’un: “Babban limamin Suleja ya rasu bayan ya dawo daga Saudiyya”

https://apahausa.com.ng/video-kai-jamaa-ku-kalli-yadda-%c6%b4a%c6%b4an-hausawa-suka-koma-tamkar-indiyawa/

Babban limamin babban masallacin Suleja a jihar Neja, Sheikh Dahiru Shuaibu, ya riga mu gidan gaskiya ranar Asabar, 22 ga watan Yuli ƴan sa’o’i kaɗan bayan ya dawo daga aikin Hajji a ƙasa mai tsarki.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani daga cikin iyalan mamacin, Abduljalil Dahiru Shuaibu, ya bayyana cewa limamin wanda ya dawo Saudiyya ranar Asabar da misalin ƙarfe 9:00 na safe, ya rasu ne sakamakon bugun zuciya da misalin ƙarfe 11:00 na dare a gidansa.

https://apahausa.com.ng/video-hadiza-gabon-ta-fa%c9%97awa-tashar-dw-kalar-mijin-da-take-son-samu-sannan-tayi-aure/

Views: 28

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *