
Dalilan da Yasa Ake Kashe Al’umma a Jihohi Biyar na Arewa~ Sheikh Zakzaky
-Jawada Mahmud Kagara (Dan Jarida)
Tun da suka shigo Nan Najeriya mu ma yanzu abin da Su ke yi Kenan.
Haka kawai mun wayi gari abin da muke Jin labari a wasu kasa she, ya zo Mana 6agatatan Mun Tabbatar ba wata kungiya wai ta kishin Islamah Wai da ake ce mata wai “Boko Haram” Mun tabbatar bata, Bata da ‘Wujudi’ sam-sam!.
A Ina? A wanne Gari? A wanne titi? A Wacce unguwa? Amma bama-bamai na tashi su suke sa bama-baman nan, ko su haka Rami wawukeke su saka su bizne su matsa rumot ko su zo da mota su Aje su danna Aikin Kenan.
Ko mutane su Bayyana su bude wuta saboda mene? Dukiya suka zo diba.
Tsakanin Zamfara ‘Zinare’ ke kwance suna son su share ‘Area’ da zinaren ke kwance ya Zama ba Mutum ko kadan su yi filin jirgin sama su yi sansanin soja su Rika Kwasar zinare.
Nan tsakanin Zaria da Birnin-Gwari ‘Zinare’ ne ke kwance da Duwatsu masu Daraja so suke su share mutane wurin su kafa filin jirgin sama su kwasa.
Tsakanin Sakoto har Zuwa Borno daga Uranium, Sai Zinare Sai Platinum shi suka so diba.
To ku zo Mana ayi ciniki koda ma ku bamu kaza mu baku rakumi, Amma ku barmu da ranmu Kuma ku Gyale Mana Addininmu.
Amma mene ne, na cewa zaku shigo ne wayo baba-rodo.
Ina ku Kuke da wayoo? Yaushe akai Ba’amerike? Yaushe akai Bature ma tukunna?
Wanne wayoo ya ke dashi? Ehmana! Dauko tarihin Bature ka karanta mana.
Badaje Maye Dan bori! Yaushe ya waye har da zai Mana wayo rashin Kunyar banza kawai.
Ku zo ayi ciniki Kuna da bindiga mun Sani Kun iya kisan Kai amma a kyale Mana Addininmu!.
LABARAI MASU ALAKA:
Yaran mu matasa da aka kashe a rikicin da ya faru tsakanin mu da sojoji a shekarar 2015 zasu dawo duniya su yi aure su haiyafa~Al-Zakzaky
Jagoran Shi’a a Najeriya Ibrahim Al-Zakzaky ya bayyana cewa iyayen yara dalibban sa da aka kashe a rikicin da ya faru a tsakanin su da sojoji a Zaria su sha kurumin su ya’yan su zasu dawo duniya nan gaba.
Al-Zakzaky ya ce ko shakka bazai yi ba, wadannan matasa zasu dawo duniya su aure su morewa rayuwar su.
©Nasara
KARIN LABARAI:

Sojojin Najeriya na ci gaba da Ragargazar ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Daga : Janaidu Amadu Doro.
Rahotanni sun bayyana cewar an kashe sama da ‘ƴan bindiga 50 tare da lalata makamansu da babura a kauyen Gidan Rijiya da ke jihar Zamfara.
Sojojin kuma sun fatataki ‘ƴan bindiga daga ginin wata makaranta da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara a wasu hare-haren sama.
Hare-haren da su ka kai ta jiragen yaƙi sun shafi yankunan Zangon Dammaka da Jajaye ma6oyar wani fitaccen ɗan bindiga Kachalla Haru da yaransa.
A cewar dakarun an yi nasarar kashe ‘ƴan bindiga da dama da lalata makamansu, sannan an lalata dazukan da su ke ɓuya a Sububu.
Views: 125
