HOTINA: “Wata Budurwar ta canza suna daga Stylish zuwa Hauwa’u bayan ta karɓi addinin Musulunci”

Wata matashiya ta karɓi addinin musulunci

𝐓𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐚 𝐛𝐚 𝐳𝐚𝐧 𝐬𝐨 𝐊𝐰𝐚𝐧𝐤𝐰𝐚𝐬𝐨 𝐝𝐚 𝐤𝐰𝐚𝐧𝐤𝐰𝐚𝐬𝐢𝐲𝐲𝐚 𝐛𝐚 ? 𝐙𝐮𝐰𝐚 𝐪𝐚𝐬𝐚𝐫 𝐰𝐚𝐣𝐞 𝐲𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐞 𝐧𝐢, 𝐡𝐚𝐫 𝐦𝐚 𝐝𝐚 𝐚𝐥’𝐮𝐦𝐦𝐚𝐫 𝐣𝐚𝐡𝐚𝐫 𝐤𝐚𝐧𝐨

1-A shekarar 2003 kafin rasuwar mahaifi na, akwai wani makusancin sa da yace a kawo takardu na gwamnatin malam Ibrahim Shekarau zata biya min kudi in je qarar Egypt in qaro karatu.

2- Daga lokacin da mahaifi na ya rasu, ko ganin wannan makusancin nasa ban qara yi ba.

3- A shekarar 2009 na gama digirin farko a fannin ilimin lissafi a jami’ar Bayero.

4- Bayan na gama bautar qasa, gwamnatin Senator Kwankwaso a shekarar 2012 ta kai ni qasar Jordan dan yin digiri na biyu bisa chanchanta da nai, ba dan na san kowa a gwamnati ba. Kuma gwamna yace idan mun samu ayyuka a Chan mu yi zaman mu.

5- Ina qasar Jordan na samu aikin koyarwa a jami’ar FUD da ke jahar Jigawa.

6-Bayan na gama digiri na biyu, saboda wayewa da na samu, cikin ikon Allah da taimakon wasu abokai mazauna qasar Turkiyya na samu gurbin digiri na uku kuma na dauki nauyin kai na karatu a qasar.

7- A qasar Turkey na hadu da wasu daga cikin shehunnan lissafi na duniya. Na shafe kusan shekaru uku a qalla a duk kwanaki biyar na cikin sati, ina karatun kusan awanni 17.

8- Na gama digiri na uku a qasar Turkey da maqaloli a fannin ilimin lissafi wadanda aka wallafa kusan 100.

9- A shekarar 2018 na dawo Nigeria dan cigaba da aiki a jam’ar FUD.

10- Na samu aiki a qasar Saudiya da kuma postdoc a qasar China. Amman na zabi in tafi China saboda wasu dalilai.

11- Na je qasar China a shekarar 2019 farko. Kuma zuwa na China shi ya bude min ido da sabgar kasuwanci. Na hadu da mutane masu daraja irin su Engr Sani Tsoho Allassan wanda shi ya fara nuna min kasuwa a qasar China.

12- Ina daga cikin yan Nigeria qalilan da qasar China ta bawa Visa mafi girma ta manyan masana da ake matuqar buqatar zaman su a China. Wannan visa ta shekaru goma qasar ta bani ni da ni da iyali na.

13- Na baro qasar China a 2020 sakamakon zuwan Covid-19.

14- Na cigaba da koyarwa ta a jami’ar FUD tare da shiga sabgar siyasa da kuma yin kasuwanci. Wanda kaso 99 na komai nawa da kasuwancin da na koyo daga China nake yi.

15-Na shiga sabgar siyasa gadan gadan a 2022 inda na rabauta da muqamin financial secretary na farko a jami’iyyar NNPP. Kuma na riqe muqamai da yawa na siyasa kafin zaben 2023. Kuma bani da buri illa in ga gwamnatin kwankwasiyya tayi nasara an cigaba da kai ya’yan talakawa qasashen waje.

16- Bayan nasarar zaben gwamna 2023, na samu ayyuka a qasashe kusan 3. Daga ciki har da qasar QATAR wacce albashin da za su bani mai kaurin gaske ne.

17- Na gama tsara tafiya ta qasar Qatar tsaf ina kan neman visa shiga qasar, mai girma gwamnan jahar Kano ya buqaci in tsaya in taya shi aiki dan cika alqawarin da yayi wa Kananawa na gyara.

18- Maigirma gwamna ya dauki muqamin Statistician General na jaha ya bani. Kuma akan wannan aikin nake yanzu.

19- Duk wadannan nasarorin idan kuka Kalle su, Sun samo asali ne daga karatun da naje qasar waje na yi. Na hadu da mutane daban daban, na samu wayewa.

20- Shi zuwa karatu qasar waje, ba wai karatun littafi kawai yake koyarwa ba, yana wayar da mutum, yana bude idanu. Kuma damar Maki suna qara yawa.

21-Jiya migirma gwamna Engr Abba K Yusuf ya cika min burina na farko, an qaddamar da tafiya karatun yara 1001. Kwana nai farin ciki. Alhamdulillah. Mungode Jagora Kwankwaso, mungode Abban Kanawa.

~Aliyu Isa Aliyu, Ph.D

Views: 18

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *